in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata tawagar gwamnatin kasar Sin za ta tashi zuwa kasar Malaysia akan bacewar jirgin sama
2014-03-10 11:27:17 cri

A safiya yau litinin 10 ga wata, wata tawagar gwamnatin kasar Sin da za ta tashi zuwa kasar Malaysia don ta kula da harkar bacewar jirgin saman kasar a zantarwar shi da manema labarai a filin jirgin sama da ke nan birnin Beijing, shugaban tawagar, kuma mataimakin darektan sashen kula da harkokin hulda da kasashen waje, Mr.Guo Shaochun ya ce, har zuwa yanzu abu mafi muhimmanci da aka sanya a gaba shi ne neman jirgin sama da ya bace tare da samar da agaji. Ya kara da cewa, tawagar za ta taimaka ma Malaysia da ma sauran sassan samar da agaji na kasa da kasa don su kara azama tare da kasar Sin wajen gudanar da aikin samar da agaji.

Mr Guo ya bayyana cewa, iyalan wasu fasinjojin kasar Sin da ke cikin wannan jirgin sama za su tashi zuwa kasar ta Malaysia bisa ga yadda kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na kasar ta shirya.

A safiyar wannan ranar ta litinin 10 ga wata, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta sanar da cewa, gwamnatin kasar ta yanke shawarar tura wata tawagar zuwa Malaysia, tawagar da ke kunshe da ma'aikatan ma'aikatar harkokin waje da na ma'aikatar tsaro da na ma'aikatar sufuri da kuma na hukumar kula da zirga-zirgar jirgen sama, don ta kula da bin sawun lamarin bacewar jirgin.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China