in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 39 suka mutu wassu 9 suka ji rauni a wani hadarin jirgin sama a Iran
2014-08-11 10:05:43 cri

Wani jirgin saman daukar fasinja ya fadi a wajen Tehran babban birnin kasar Iran a safiyar Lahadin nan tare da hallaka mutane 39 wassu guda 9 kuma suka ji rauni, kamar yadda gidan talabijin din kasar IRIB ta ba da rahoto.

Jirgin mai suna Antonov-140 ko Iran 140 na kamfanin jiragen saman Sepahan yana da niyyar zuwa birnin Tabas ne dake kudancin kasar, amma sai ya fadi jim kadan da tashinsa daga babban filin jiragen saman na Mehrabad da misalin karfe 10 saura kwata na safiyar agogon kasar.

Tun da farko dai sai da kafar yada labarai ta sanar da cewa, dukkannin mutanen da ke cikin jirgin su 48 da suka hada da fasinjoji 40 da ma'aikatan jirgin 8 sun hallaka, bayan da jirgin ya fadi a wata unguwa mai dauke da gidajen jama'a na Azadi mai tazarar kilomita 5 daga yammacin birnin na Tehran.

Wadanda suka mutu dai ba'a tabbatar da ko su wane ne ba saboda konewar da suka yi yadda gane su farat daya ke da wuya, amma za'a tantance su bayan an yi gwajin zamani na DNA, inji kafar talabijin din kasar.

Wani ganau a hadarin ya sheda ma kamfanin dillancin labarai na FARS cewa, ya ga sadda jirgin ya rabu gida biyu bayan da ya daki katangar kankare, wutsiyar ya fita ya fadi waje daya a kan titi kusa da ma'aikatar sarrafa gilas na Mina dake birnin na Azadi.

Kamfanin dillancin labarai na FARS ya ruwaito Mohammed Ilkhani shugaban kamfanin jiragen saman na Iran na cewa, matsalar da aka samu a daya daga cikin injin din jirgin ya haddasa faduwarsa a arewacin babban hanyar Tehran zuwa Karaj.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China