Shugaban jam'iyyar mai ra'ayin sassauci ta kasar Masar kuma tsohon dan takarar zaben shugaban kasar a shekarar 2012 Hamdeen Sabahi ya sanar da shiga zaben shugaban kasar a jiya Asaba 8 ga wata a birnin Alkahira. Wannan shi ne mutum na farko da ya bayyana shiga zaben a wannan karo. A gun wani taron manema labarai, mista Sabani ya nanata cewa dalilin mutuntawar da yake nunawa 'yan sanda da rundunar sojan kasar, ya bashi karfin shiga wannan zabe bisa sunan "juyin juya hali". Kafin wannan kuma, Sabahi ya taba nuna cewa, idan shugaban sojan kasar Abdel Fatah Al-Sisi ya sanar da shiga zaben, zai goyi masa baya.
Ya zuwa yanzu, babban kwamitin sojan kasar ya yarda da Sisi da ya shiga zabe, amma har yanzu Sisi bai mayar da martani ba kan wannan kira.
A tsakiyar watan da ya gabata, aka zartas da sabon daftarin tsarin mulkin kasar bisa kuri'u mai rinjiaye sosai. A ran 26 ga watan Jarairu kuma, shugaban wucin gadi Adly Mansour ya sanar da cewa, za a gudanar da zaben shugaban kasar kwanaki 30 zuwa 90 bayan da aka fara amfani da sabon tsarin mulkin kasar. (Amina)