Lauyan jam'iyyar 'yanuwa Musulmai ta kasasr Masar (MB) Adel-Moneim Abdel-Maqsood ya nuna a ran 4 ga wata cewa, ya zuwa yanzu, jam'iyyar tana bincike kan matakan shari'a da mambobinta wadanda ake tsare da su za su fusakanta, don haka ba ta yanke shawarar daukar karin mataki ba tukuna.
A daren wannan rana kuwa, sojojin kasar sun ba da wata sanarwa cewa, bangaren soja ba za ta dauki matakai na musamman kan jam'iyyau da kungiyoyin siyasa.
Ban da haka, Adel-Moneim Abdel-Maqsood ya musanta cewa, an tasa keyar Mohammed Morsy zuwa hukumar tsaron kasar, yana mai cewa, yanzu rundunar tsaron kasar ta yi masa daurin talala.
Rundunar tsaron kasar ta tsare manyan jami'an biyu na jam'iyyar 'yanci da adalci dake karkashin jam'iyyar MB a daren ranar 3 ga wata. Bisa labarin da shafin Intanet na jaridar Al-Ahram ta bayar, rundunar na shirin tsare wasu sauran mambobin jam'iyyar MB 300. (Amina)