in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fadar shugaban kasar Masar ta ce shiga tsakanin da kasashen duniya suka yi ya ci tura
2013-08-08 16:38:36 cri

Fadar shugaban kasar Masar ta sanar a ran 7 ga wata cewa, shiga tsakanin da kasa da kasa suka yi tsakanin gwamnatin wucin gadi ta Masar da jam'iyyar 'yan uwa musulmi da dai sauran kungiyoyin musulmi ya ci tura.

Fadar ta ba da wata sanarwa a wannan rana cewa, an kawo karshen neman masalaha ta hanyar diplomasiyya, yanzu Masar za ta shiga wani "sabon matakin'' warware rikicin kasar. Sanarwar ta bayyana cewa, ko da yake shiga tsakanin da kasa da kasa suka yi ya sami babban goyon baya daga gwamnatin wucin gadi ta kasar, amma har ila yau yunkurin kasa da kasa na neman samun sulhu ya kasa cimma nasara, amma duk da haka, kasar Masar na fatan bangarori da wannan abin ya shafa za su ci gaba da kokarin da suke yi kan shirin mika mulkin kasar cikin lumana ta hanyar demokaradiya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China