in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojin kasar Masar sun sanar niyyar gudanar da babban zabe kafin lokacin da aka kayyade
2013-07-04 11:21:57 cri

Ministan tsaron kasar Masar Janar Abdelfattah al Sisi ya ba da jawabi ta gidan telabijin a daren ranar 3 ga wata, inda ya sanar nada shugaban babban kotu a matsayin sabon shugaban kasar na rikon kwarya gami da gudanar da babban zabe kafin lokacin da aka kayyade.

Janar Abdelfattah al Sisi ya ce, shirin taswirar da sojojin kasar suka gabatar wajen raya kasar nan gaba ya kunshi bangarori hudu, dakatar da tsarin mulki na yanzu, yin zaben shugaban kasar da kuma sanya shugaban babban kotu ya yi rikon kwaryan shugabancin kasar har a fito da sabon shugaba, kafa wata gwamnatin hadin kai, da kuma kafa wani kwamiti don yi wa tsarin mulki kwaskwarima.

Janar Abdelfattah al Sisi yana mai cewa, an ci tura ne kan shawarwarin tsakanin sojojin kasar da shugaba Mohamed Morsy, kuma jawabin da Morsy ya bayar a ran 2 ga wata bai samu amincewa daga jama'a ba. Janar Abdelfattah al Sisi kuma ya jaddada cewa, sojojin kasar ba za su yi biris da bukatun jama'a ba, amma ba zai shiga hakar siyasa ba har abada.

A tsakar daren laraba 3 ga wata, Mohamed Morsy ya yi jawabi ta gidan talabijin domin nanata matsayinsa na shugaba bisa doka tare kuma da jaddada cewa, babu wani abu da zai maye gurbin tsarin mulki da doka yanzu. Kafin ya ba da wannan jawabi, Morsy ya nuna cewa, abin da Sisi suka yi tamkar juyin mulkin soja ne. Kuma ya yi kira ga dukkan jama'ar da su bi shari'a da doka yadda ya kamata, bai kamata su goyi bayan juyin mulkin da aka yi ba.

Game da sauyin halin da ake ciki a kasar Masar, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ba da wata sanarwa a ran 3 ga wata, inda ya yi kira ga sojojin Masar da ya zabi shugaban kasar bisa tsarin dimokuradiyya yadda ya kamata a kasar ta yin amfani da tsari mai adalci cikin lokaci, tare kuma kauracewar tsare Morsy da magoyansa ba tare da yin tunani mai zurfi ba.

Ban da haka, babbar wakiliya ta kungiyar tarayyar kasashen Turai EU kan manufofin diplomasiyya da tsaro Catherine Ashton ta ba da sanarwa a ran 3 ga wata kan halin Masar, inda ta kalubalanci bangarori daban-daban na kasar da su yi hakuri da juna da nanata wajibcin bin ka'idar zaman lafiya da daina nuna karfin tuwo. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China