in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An karyata batun nadin El-Baradei a matsayin Firaminstan kasar Masar
2013-07-07 16:24:46 cri
Mahukunta a Masar sun karyata rade-radin da ake yi cewa wai an bayyana sunan babban dan adawar kasar Mohamed El-Baradei a matsayin firaministan kasar na rukon kwarya.

Rahotannin baya-bayan nan da kamfanin dillancin labaran kasar ta Masar MENA ya fitar, sun rawaito mai baiwa shugaban kasar shawara ta fuskar watsa labarai Ahmed Al-Mislimani, na bayyyana cewa ko alama, shugaban rikon kwaryar kasar Adli Mansour bai nada wani a mukamin na firaminista ba, koda yake yace kawo yanzu ana ci gaba da tattaunawa don gane da wanda za a dorawa wannan nauyi.

Mislimani ya kara da cewa tattaunawar da ake yi ta kunshi manyan wakilan siyasar kasar, ciki hadda shi kansa El-Baradei, da Abdel-Moneim Aboul-Fotouh, shugaban jam'iyyar Strong Egypt Party, da Galal Murra na jam'iyyar Nour, da wakilan gungun masu zanga-zangar da ta sabbaba tumbuke gwamnatin shugaba Morsi, da ma sauran masu fada a ji.

Fitar jita-jitar nadin firaministan dai ta yamutsa hazo tsakankanin masu ruwa da tsaki, inda jam'iyyar Al-Nour da tsagin siyasa na kungiyar 'yan uwa musulmi wato "Freedom and Justice party" suka yi watsi da batun nadin, matakin da suka ce zai dada munana halin da ake ciki a kasar.

Don gane da batun kokarin da gwamnatin rikon kwaryar kasar ke yi na lalubo hanyar warware matsalolin dake akwai, Mislimani yace ba za a nunawa wani bangare wariya ba. Game da batun kame wasu magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi da wasu jagororin masu ra'ayin Islama kuwa da aka yi, mai baiwa shugaban kasar shawara yace anyi hakan ne bisa tanajin doka, ba kuma a yi hakan bisa dalilai na siyasa ba. (Saminu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China