in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban rikon kwarya a kasar Masar ya jaddada cewa, kowace jam'iyya na iya yin sulhu tsakanin al'umma
2013-07-19 11:04:10 cri

Shugaban rikon kwarya na kasar Masar Adly Mansour ya ba da jawabi ta telibijin a ran 18 ga wata, inda ya jaddada cewa ko wace jam'iyya da kungiyar siyasa na iya yin sulhu da ake yi tsakanin al'umma.

A cikin jawabinsa, Adly Mansour yana mai cewa, bisa bukatun jama'ar kasar, firaministan wucin gadi Hazem Beblawi ya cimma nasarar kafa wata ''majalisar ministoci ta masana'' domin dukufa kan magance kalubalolin da kasar ke fuskanta yanzu, kuma ya gayyaci dukkan kungiyoyin siyasa da hukumomi don tabbatar da adalci da sulhu a duk kasar bisa tushen siyasa da zama tare cikin lumana. Ya bayyana cewa, kasar Masar na tinkarar wani muhimmin lokaci yanzu, kuma gwamnatin wucin gadi za ta yi iyakacin kokarinta na kiyaye tsaron kasar da zaman karko na al'ummar.

A ganin Adly Mansour, zanga-zanga da jama'ar kasar suka yi a watan Janairu na shekarar 2011, da na watan Yuni zuwa watan Yuli na shekarar bana, sun jawo hankalin mutanen duniya sosai, amma wannan ba zai yi wa kasar wani tabo ba a idon kasashen duniya, muddin gwamnatin wucin gadi ta farfado da tattalin arzikin al'umma da daga matsayin zaman rayuwar jama'a. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China