Cikin sanarwar, Ban Ki-Moon ya nuna goyon baya ga ikon jama'ar kasar Masar wajen yin zanga-zanga cikin lumana, ya kuma yi kira ga gwamnatin wucin gadi ta kasar da ta tabbatar da dokokin shari'a da oda, sa'an nan kuma ta kiyaye tsaron al'umman kasar, a kuma daina kama mutane ba tare da wata hujja ba, kana ya kamata gwamnatin ta saki shugaba Mohamed Morsy wanda aka hambarar daga mukaminsa da ma sauran shugabannin kingiyar 'yan'uwa Musulmi ba tare da bata lokaci ba, sa'annan ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Bayan rundunar sojan kasar Masar ta hambarar da Mohamed Morsy daga mukaminsa ran 3 ga watan nan da muke ciki, ana ci gaba da samun rikice-rikice tsakanin jam'iyyu daban daban na kasar.
Sakamakon haka, a ran 25 ga wata, rundunar sojan kasar ta yi gargadi ga jam'iyyar 'yan'uwa Musulmi da ta shiga shawarwari na duk kasa baki daya cikin awoyi 48, in ba haka ba, rundunar sojan kasar za ta dauki matakai don yaki da aikace-aikacen tashin hankali da na 'yan ta'adda a kasar. (Maryam)