Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na MENA ya bayar, an ce, a wannan rana, magoya bayan Morsy sama da dari daya sun yi artabo da masu adawa da shi a kusa da wani masallaci a jihar Alexandria dake arewacin Masar, wanda ya haddasa mutuwar mutum daya, yayin da wasu mutane biyar suka jikkata, sannan aka cafke wasu da dama daga cikinsu.
Daga ranar 14 ga watan Agusta na bana, bayan da gwamnatin Masar ta kawar da manyan sansanonin zanga-zanga biyu na magoya bayan Morsy, tare da cafke membobin kungiyar 'yan uwan Musulmi a ko wace ranar Jumma'a a duk fadin kasar magoya bayan Morsy na gudanar zanga-zanga, lamarin dake janyo rikici tsakanin da masu adawa da Morsy da sojoji da 'yan sanda a kai a kai.
A wannan rana kuma, mai daukaka kara na Masar ya shelanta cewa, game da tuhumar da ake masa na neman tserewa daga gidan kurkuku da lekan asiri da sauransu, za a kara wa'adin tsare Mohamed Morsy har na tsawon kwanaki 30.(Fatima)