Yayin wata tattaunawa da ya yi ta wayar tarho ranar Lahadi 28 ga wata, da mataimakin shugaban kasar ta Masar Mohamed El-Baradei, Mr. Ban ya bayyana rashin gamsuwarsa da yadda al'amura ke wakana a kasar, yana mai bayyana matukar bukatar da ake da ita ga mahukuntan kasar na daukar matakan da suka dace, don warware matsalolin siyasar kasar ta hanyar lumana.
Daga nan sai ya nanata bukatar sakin tsohon shugaban kasar Mohammed Morsi, wanda mahukuntan kasar kewa daurin talala, tare da ragowar magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi da aka kame, ko kuma a tabbatar da gudanar da bincike kan su bisa tsari na adalci.
A wani ci gaban kuma shugaban kasar ta Masar na rikon kwarya Adli Mansour, ya bayyana amincewarsa da baiwa Firaministan kasar Hazem Beblawi wani yanki na ikonsa, don gane da batun daukar matakan dake kunshe cikin dokar ta baci, matakin da ake ganin zai iya baiwa Beblawi damar umartar sojoji su damke, tare da tsare fararen hula, musamman wadanda ake gani na zamewa gwamnatin rikon kwaryar kasar kadangaren bakin tulu. (Bello Wang)