A wannan rana, masu goyon bayan Morsy sun yi taru a birnin Alkahira don yin zanga-zanga, inda sakamakon haka, an samu matsalar zirga-zirgar motoci a wasu yankunan dake birnin. An jibge sojojin kasar a muhimman wuraren da suka yi zanga-zanga, kana an kange wasu hanyoyin motoci.
A wannan rana da yamma a wajen masallacin Azhar, masu goyon bayan Morsy da masu adawa da shi sun yi arangama, amma babu wanda ya ji rauni. A maraicen ranar, masu goyon bayan Morsy sun yi rikici tare da bangaren soja na kasar a dab da fadar shugaban kasar, kuma 'yan sanda sun harba barkonon tsohuwa ga masu zanga-zanga.
Ban da birnin Alkahira, masu goyon bayan Morsy sun yi zanga-zanga a birnin Alexandria, Mansoura da sauran biranen kasar, an kuma samu rikice-rikice a wasu wurare. Bisa labarin da aka bayar, an ce, mutane a kalla 2 sun mutu kana mutane 7 sun ji rauni a sakamakon rikicin da aka samu a birnin Mansoura na kasar. (Zainab)