in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matakin da aka dauka domin tarwatsa 'yan zanga-zanga ya haddasa hasarar rayuka ko jikkata a kasar Masar
2013-08-15 15:16:19 cri

Sojojin kasar Masar sun tarwatsa sansanonin magoya bayan Mahmoud Morsy a ran 14 ga wata a filaye biyu da ke birnin Alkahira, inda lamarin ya yi sanadin asarar rayuka da raunata jama'a. Hakan ya sa, gwamnatin wucin gadi ta kasar ta sanar da kafa dokar ta baci har tsawon wata daya.

Bayan sojojin sun kori masu zanga-zanga, kungiyar 'yan uwa musulmi ta yi kira ga karin mambobinta da masu goyon bayan Morsy da su yi zanga-zanga domin nuna rashin jin dadi ga rundunar tsaro. A wannan rana kuma, masu zanga-zanga sun cinna wuta kan motoci ko itatuwa a wasu larduna, sun kuma kutsa kai cikin ginin gwamnatin kasar da kai hari kan ofishin 'yan sanda. Har ila yau, rikici na bazuwa a duk fadin kasar.

Kakakin ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ya bayyana a ran 14 ga wata cewa, ya zuwa yanzu, mutane a kalla 278 sun mutu sakamakon rikicin, yayin da wasu fiye da 2000 sun samu rauni. Ministan harkokin cikin gida na kasar Mohamed lbrahim ya kira wani taron manema labaru a daren wannan rana cewa, inda ya baiyana cewa 'yan sanda a kalla 43 sun mutu kuma 211 suka jikkata cikin matakin da sojojin suka dauka.

Telibijin na kasar ya ruwaito sanarwar da fadar shugaban kasar ta bayar na cewa, kasar ta shiga halin dokar ta baci daga karfe 4 na ran 14 ga wata da yamma har na tsawon wata daya. Ban da haka, an ba da labari cewa, an hana fitar dare daga karfe 7 na ran 14 ga wata da dare zuwa karfe 6 na ran 15 ga wata da safe. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China