A ranar Larabar da ta gabata ne dai ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta fidda wata sanarwa, wadda ta bayyana yanke shawarar daina baiwa kasar Masar din wani sashe na taimako, har ya zuwa lokacin da kasar za ta kai ga gudanar da zabe cikin 'yanci da adalci, ta kuma kafa gwamnati bisa burin jama'arta.
Dangane da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar Badr Abdel, ya yi tir da shawawar da Amurka ta yanke, ta janye wani tallafi da take baiwa kasarsa. Abdel wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis 10 ga watan nan ya ce, daukar wannan mataki kuskure ne da Amurka ta yi.
Da yake karin haske kan matsayar kasar tasa, Badr Abdel ya ce yanke wannan hukunci zai sanya a aza ayar tambaya game da manufar taimakon da Amurka ke samarwa, da kuma burinta game da tsaron kasar Masar, musamman ma a wannan lokaci da kasar ke fuskanta kalubaloli da suka hada da na ayyukan ta'addanci.
Duk da haka Abdel ya ce, Masar na fatan kiyaye dangantakar dake tsakaninta da Amurka, sai dai ya tabbatar da cewa Masar tana son daidaita harkokinta da kanta ba tare da sa hannun kasashen waje ba, musamman harkokin da suka shafi tsaron kasar. (Amina)