A ranar Lahadi, bisa wani yunkuri, shugaban mulkin wucin gadi Adli Mansour ya gabatar da wani kuduri, wanda janyo jita jitar mutane dake bayyana cewa wannan kuduri zai kasance wani mafarin farautar 'yan gani kashenin shugaba Mohamed Morsi, da suka fara kai hare hare kan jami'an tsaro a yankin Sinai.
Amma kuma mista Mislimani ya bayyana cewa wannan mataki na shugaba Adli Mansour an dauke shi ne bisa manufar cimma ikon kasa. Duk da kawar da zancen dake nuna cewa wannan doka zata fara aiki cikin gaggawa, mashawarcin shugaban kasa ya jaddada cewa wasu abubuwan tashe tashen hankali da suka faru na baya baya na bukatar ganin an kafa wannan mataki domin kiyaye zaman lafiyar kasa. (Maman Ada)