A ranar Alhamis 12 ga wata ne gwamnatin wucin gadi na kasar Masar ta yanke shawarar kara lokacin dokar ta baci da ake tafiyar da ita a duk kasar har zuwa watanni biyu masu zuwa.
Kakakin fadar shugaban kasar Ihab Al-Badawi ya sanar a yammacin wannan rana cewa, Shugaba Adly Mansour ya yanke wannan shawara ne bisa halin tsaro da ake ciki a kasar, kuma karin lokacin da aka yi ya fara ne tun daga karfe 4 na yamma na wannan rana.
'Yan sandan kasar sun dauki mataki tarwatsa masu zanga-zanga magoya bayan Morsy a wasu wurare biyu na birnin Alkahira a ran 14 ga watan Agusta da ya gabata. Daga baya kuwa, shugaban rikon kwarya Adla Mansour ya sanar da kafa dokar ta baci har na tsawon wata daya daga karfe 4 na yammacin ranar 14 ga watan da ya gabata.
Bisa sanarwar ta Shugaba Mansour ya bayar game da kundin tsarin mulkin kasar an ce, ba za a iya kara tsawaita lokacin dokar ta baci ba, face sai ta hanyar kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a muddin aka kawo karshen halin dokar na tsawon watanni uku. (Amina)