A wannan rana, kakakin sojan kasar Ahmed Mohammed Ali ya sanar da cewa, an kai farmaki a sansanin ne da karfe 9 na daren ranar 10 ga wata. Rundunar sojojin ta kuma murkushe wani siton da dakaru suka ajiye makamai a lokacin farmakin. Ya kuma kara da cewa, za a ci gaba da daukan matakai irin haka ga dakarun da ke makurdadar Sinai. Wadannan 'yan ta'adda da sojojin kasar suka kai wa hari a wannan karo sun taba kashe sojoji da 'yan sandan kasar a lardin arewacin Sinai.
Tun lokacin da aka hambarar da Mohamed Morsy, ake ta fama da rikice-rikice a kasar. Kuma mutane da dama sun rasu ko jikkata a sanadiyyar hare-haren da 'yan ta'adda suka kai a wasu tashoshin yin bincike da kuma ofisoshin 'yan sanda da suke makurdadar Sinai, wato wurin iyakar dake tsakanin kasar Masar da ta Isra'ila. Ran 27 ga watan Yuli, rundunar sojojin kasar Masar ta fara aikace-aikacen yaki da 'yan ta'adda da masu tada zaune tsaye a makurdadar Sinai. (Maryam)