A cewar jaridar Pyramid ta kasar Masar, zargin da ake yi ma Morsy ya hada da laifin leken asirin kasa, hada kai da kungiyar Hamas domin kai hari ga gidan kaso, sace da kuma kashe wasu jami'an tsaro da ma wasu fursunoni.
Labarin da aka bayar ya sheda cewa, kotun kolin kasar Masar ta riga ta fara bincike kan zargin da ake yi wa Mohamed Morsy, wadda kuma ta yi umarnin tsare shi cikin gidan wakafi har kwanaki 15. Daga bisani, Mista Morsy zai fuskanci shari'ar da za a yi don tantance ko ya hada kai da kungiyar Hamas a shekarar 2011 don a kai hari ga ofishin 'yan sanda da bude gidan yari, ko a'a. (Bello Wang)