Tun 14 ga wata, gwamnatin kasar Masar ta sanar da dokar hana fitar dare tun karfe 7 na dare zuwa karfe 6 na safe a larduna 14 wadanda ke fama da tashin hankali. Kan lamarin, kafofin watsa labaran kasar suna ganin cewa, gwamnatin wucin gadin kasar ta sassauta lokacin dokar hana fitar dare don halin dokar ta baci na kyautatuwa a halin yanzu.
Ran 23 ga wata, ba a samu yawan mutanen masu zanga-zanga kamar a kwanakin baya, haka kuma yawan mutanen da suka jikkata ko rasu ya ragu cikin zanga-zanga da kawancen magoya bayan tsohun shugaban kasar Mohamed Morsy ya tashe.
Jaridar Al-Ahram ta ruwaito maganar wasu masana cewa, dalilan biyu da suka sa yawan mutanen da suka shiga zanga-zanga ya ragu kwanan baya, su ne, hukumar tsaron kasar ta kama shugabanni da dama na kungiyar 'yan uwan Musulmi, na biyu shi ne, bayan shekara daya shugabancin Mohamed Morsy, jama'ar kasa sun riga sun rasa halayen jin tausayi da kuma goyon baya kan kungiyar 'yan uwan Musulmi.( Maryam)