Kwamitin zabe na kasar Masar ya sanar a Asaba 18 ga wata cewa, an zartas da sabon kundin tsarin mulkin kasar na zaben raba gardama da aka yi daga ran 14 zuwa 15 ga watan da muke ciki, da kashi 98.1 cikin dari na yawan kuri'un da aka jefa.
A gun taron manema labaru da aka yi a wannan rana da dare, shugaban kwamitin Nabil Salib ya sanar da cewa, yawan mutane dake da hurumin shiga zabe ya kai kimanin miliyan 53.4, sai dai wadanda suka shiga zabe ya kai miliyan 20.61. Yawan kuri'un amincewa da sabon kundin tsarin mulkin ya kai miliyan 19.985 wanda ya kai kashi 98.1 bisa dari na dukkan kuri'un da aka kada, yayin da yawan kuri'un kin amincewa ya kai kashi 1.9 cikin dari kawai. (Amina)