Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
 
• Za a gudanar da dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka 2009-11-05
Daga ran 8 zuwa ran 9 ga watan Nuwamba na bana, a birnin Sharm El Sheikh na Masar, za a gudanar da taron ministoci a karo na 4 na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Wannan shi ne gagarumin taro da za a yi bayan taron koli na birnin Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a shekarar 2006
• Za a yi zaben shugaban kasa a zagaye na biyu a kasar Afghanisan 2009-10-21
A ran 20 ga watan nan hukumar zabe mai zama kanta ta kasar Afghanistan ta sanar da cewa za a yi zaben shugaban kasa a zagaye na biyu a ran 7 ga watan Nuwanba a kasar saboda daga cikin 'yan takara babu wanda ya samu rabin kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasa da aka yi ran 20 ga watan Augusta.
• Ana ci gaba da fama da halin rashin tabbas a kasar Madagascar 2009-10-08
A ran 6 ga wata da dare a birnin Antananarivo, manyan jam'iyyun siyasa hudu na Madagascar sun cimma daidaito a kan raba muhimman mukamai na gwamnatin wucin gadi ta kasar, abin kuma da ya share fagen samun sulhu a kasar. Amma duk da haka, ana ci gaba da shakkar ko bangarori daban daban na kasar za su iya tabbatar da daidaiton da suka cimma.
• Ba'a cimma tudun-dafawa ba a yayin shawarwarin Palesdinu da Isra'ila gami da Amurka 2009-09-23
Ranar 22 ga wata, a birnin New York na kasar Amurka, shugaban kasar Barack Obama ya yi shawarwari tare da firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu, da shugaban al'ummar Palesdinawa Mahmoud Abbas wadanda suka halarci babban taro a karo na 64 na Majalisar Dinkin Duniya
• Bikin tunawa da kafuwar jamhuriyar Libya 2009-09-10
Ranar 1 ga watan Satumba, a kasar Libya, an kaddamar da bikin tunawa da kafuwar jamhuriyar kasar Libya a shekaru 40 da suka wuce, inda aka shirya gagaruman bukukuwa cikin makon da ya biyo baya. Shugabannin kasashe daban daban sun halarci bikin, haka kuma an shirya wani taron koli na musamman na kungiyar gamayyar kasashen Afirka ta AU a birnin Tripoli, fadar mulkin kasar Libya.
• Gardama na kara tsanani kan zaben shugaban kasa a Afghanistan 2009-08-26
Ran 25 ga wata, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Afghanistan ta bayar da sakamakon zaben shugaban kasa a karo na farko, cewa Hamid Karzai, shugaban kasar Afghanistan na yanzu yana kan gaba da rinjaye kadan. A sa'i daya kuma, ana ci gaba da gardama kan magudin da aka samu a cikin zaben shugaban kasar.
• Hillary ta kalubalanci gwamnatin Kongo Kinshasa da ta kare 'yan mata don kada a ci zarafinsu 2009-08-12
An labarta cewa, sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka Madam Hillary Clinton ta tashi daga birnin Kinshasa, hedkwatar Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo kuma ta sauka a birnin Goma, hedkwatar lardin Kivu ta Arewa da ke gabashin kasar a ranar 11 ga wata cikin jirgin saman Majalisar Dinkin Duniya, inda ta yi shawarwari tare da shugaban kasar Kongo Kinshasa Joseph Kabila.
• Ya kamata kasar Amurka ta kara yin hakuri, in ji bangaren Isra'ila 2009-07-29
Daga ranar 27 ga watan Yuli, wasu manyan kusoshin gwamnatin kasar Amurka, wadanda suka hada da Robert Gates, ministan tsaron kasar, da George Mitchell, manzon musamman na kasar kan batun gabas ta tsakiya, sun kai ziyara a yankin gabas ta tsakiya daya bayan daya, inda suka sa kaimi ga bangarorin da abun ya shafa don su yi kokarin shimfida zaman lafiya a gabas ta tsakiya.
• Har wa yau dai makomar tattalin arzikin Amurka tana cikin  halin rashin sanin tabbas 2009-07-15
Har wa yau dai makomar tattalin arzikin Amurka tana cikin halin rashin sanin tabbas Assalamu alaikun jama'a masu sauraro, barkanku da war haka,barkanmu da sake saduwa da ku a wannan shirin na duniya ina labari. A cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wani bayanin da wakilin gidan rediyo ya ruwaito mana a kan cewa har yanzu dai makomar tattalin arzikin Amurka tana cikin halin rashin sanin tabbas.
• Taron koli na AU na mai da hankali kan batun bunkasa ayyukan gona da kuma halin da ake ciki a Somaliya da dai sauran muhimman batutuwa 2009-07-02
An bude taron koli na 13 na yini 3 na kungiyar kawancen kasashen Afrika wato AU a ranar 1 ga wata a birnin Sirte dake bakin tekun kasar Libya, wanda ya samu hallarar shugabannin kasashe da na gwamnatoci ko kuma wakilai na kasashe sama da 50 na Nahiyar Afrika. A gun wannan taro, kasashe membobi daban daban na kungiyar AU za su yi tattaunawa kan yadda za a sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki ta fuskar kara saka jari a fannin noma,
1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17