Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-23 18:14:20    
Ba'a cimma tudun-dafawa ba a yayin shawarwarin Palesdinu da Isra'ila gami da Amurka

cri

Ranar 22 ga wata, a birnin New York na kasar Amurka, shugaban kasar Barack Obama ya yi shawarwari tare da firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu, da shugaban al'ummar Palesdinawa Mahmoud Abbas wadanda suka halarci babban taro a karo na 64 na Majalisar Dinkin Duniya, amma bangarorin uku ba su cimma maslaha ba a yayin shawarwarin. Manazarta suna ganin cewa, a halin yanzu da wuya ainun Palesdinu da Isra'ila su cimma matsaya a kan batun farfado da shawarwarin shimfida zaman lafiya, makomar sake maido da shawarwari tsakanin bangarorin biyu tana kasa tana dabo.

Bayan shawarwarin, Benjamin Netanyahu ya bayyanawa kafofin watsa labarai cewa, shugabannin bangarorin uku, wato Palesdinu, da Isra'ila, gami da Amurka sun amince da a farfado da yunkurin wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya tun da wuri, amma ba su cimma daidaito ba kan karin batutuwa. A nasa bangare kuma, shugaban al'ummar Palesdinawa Mahmoud Abbas ya bayar da wata sanarwa bayan shawarwarin, inda ya ce, a yayin shawarwarin, al'ummar Palesdinawa ta sake jaddada bukatarta ta daina ayyukan gina matsugunan Yahudawa da kasar Isra'ila ke yi.

1 2 3