Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-29 16:45:21    
Ya kamata kasar Amurka ta kara yin hakuri, in ji bangaren Isra'ila

cri

Daga ranar 27 ga watan Yuli, wasu manyan kusoshin gwamnatin kasar Amurka, wadanda suka hada da Robert Gates, ministan tsaron kasar, da George Mitchell, manzon musamman na kasar kan batun gabas ta tsakiya, sun kai ziyara a yankin gabas ta tsakiya daya bayan daya, inda suka sa kaimi ga bangarorin da abun ya shafa don su yi kokarin shimfida zaman lafiya a gabas ta tsakiya. Cikin kwanakin da suka wuce, gwamnatin kasar Amurka ta lallashi tsohuwar kawarta, kasar Isra'ila, tare da yi mata matsin lamba, amma duk da haka, ba a san wane irin rangwame gwamnatin kasar Isra'ila mai tsatsauran ra'ayi ka iya samarwa ba tukuna, haka kuma ba a tabbatar da lokacin da za a aiwatar da matakin ba. Kamar dai yadda Shimon Peres, shugaban kasar Isra'ila, ya gaya wa George Mitchell, manzon musamman na gwamnatin kasar Amurka kan batun gabas ta tsakiya, cewar ya kamata kasar Amurka ta kara yin hakuri kan batun.
1 2 3