Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-02 10:49:00    
Taron koli na AU na mai da hankali kan batun bunkasa ayyukan gona da kuma halin da ake ciki a Somaliya da dai sauran muhimman batutuwa

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, an bude taron koli na 13 na yini 3 na kungiyar kawancen kasashen Afrika wato AU a ranar 1 ga wata a birnin Sirte dake bakin tekun kasar Libya, wanda ya samu hallarar shugabannin kasashe da na gwamnatoci ko kuma wakilai na kasashe sama da 50 na Nahiyar Afrika. A gun wannan taro, kasashe membobi daban daban na kungiyar AU za su yi tattaunawa kan yadda za a sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki ta fuskar kara saka jari a fannin noma, da tabbatar da tsaron abinci, da halin da ake ciki yanzu a kasar Somaliya da wassu muhimman batutuwan da suka shafi kasashen Afrika da kuma batun kafa hukumar iko ta kungiyar AU da dai sauransu.

Jama'a masu sauraro, kowa ya san cewa, sha'anin noma ya kasance wata sana'ar ginshiki ta kasashen Afrika, wadanda kuma suke dogaro da ita wajen samun bukasuwar tattalin arziki da kuma kawar da talauci. Bisa abubuwan da aka tanada cikin wani ' Rahoto kan harkokin tattalin arzikin kasashen Afrika a shekarar 2009' da kwamitin kula da harkokin tattalin arzikin kasashen Afrika na Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar tarayyar Afrika suka gabatar da shi cikin hadin gwiwa a watan da ya gabata, an ce, har wa yau dai, sha'anin noma na tsayawa kan matsayin jagoranci na ayyukan bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika, wato ke nan kimanin kashi 25 zuwa kashi 35 cikin kashi 100 na yawan GDP, da kuma kimanin kashi 60 cikin kashi 100 na yawan kudin shiga na masu samun aikin yi da na manoma sukan zo ne daga fannin sha'anin noma. Sanda ake fuskantar tarzomar abinci da kuma rikicin hada-hadar kudi na duniyan, kasashen Afrika suka fi gane cewa, sha'anin noma, wani babban lamari ne dake shafar ayyukan samun bunkasuwa da kuma kwanciyar hankali na Nahiyar Afrika. Dole ne a dauki tsauraran matakai don samun ci gaba.

1 2 3