Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-26 17:09:56    
Gardama na kara tsanani kan zaben shugaban kasa a Afghanistan

cri

Ran 25 ga wata, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Afghanistan ta bayar da sakamakon zaben shugaban kasa a karo na farko, cewa Hamid Karzai, shugaban kasar Afghanistan na yanzu yana kan gaba da rinjaye kadan. A sa'i daya kuma, ana ci gaba da gardama kan magudin da aka samu a cikin zaben shugaban kasar. Wasu mutane suna damuwa watakila wannan gardama za ta kawo tangarda ga halin da Afghanistan ke ciki.

Ran 25 ga wata, Daud Ali Najafi direkatan hukumar zabe ta kasar Afghanistan ya sanar da cewa, bisa kuri'un da aka kidaya na kashi 10 daga cikin kashi 100 na dukkan kuri'un da aka jefa, akwai cikakkun kuri'u dubu 524, Hamid Karzai ya sami kashi 40.6 cikin 100, Abdullah Abdullah, tsohon ministan harkokin waje ya sami kashi 38.7 cikin 100, Ramazan Bashardost 'dan majalisa ya sami kashi 10.2 cikin kashi 100, kuma Ashraf Ghani tsohon ministan harkokin kudi ya sami kashi 3 cikin kashi 100. hukumar zabe ta yi alkawarin cewa, a cikin kwanaki masu zuwa, za ta sanar da wasu sakamakon zabe a ko wace rana, kuma za a sanar da sakamakon babban zabe na karshe a wata mai zuwa.

1 2 3