Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-12 13:26:08    
Hillary ta kalubalanci gwamnatin Kongo Kinshasa da ta kare 'yan mata don kada a ci zarafinsu

cri

An labarta cewa, sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka Madam Hillary Clinton ta tashi daga birnin Kinshasa, hedkwatar Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo kuma ta sauka a birnin Goma, hedkwatar lardin Kivu ta Arewa da ke gabashin kasar a ranar 11 ga wata cikin jirgin saman Majalisar Dinkin Duniya, inda ta yi shawarwari tare da shugaban kasar Kongo Kinshasa Joseph Kabila. A lokacin shawarwarin, Madam Hillary ta nuna damuwa sosai kan yadda ake cin zarafin 'yan mata da kananan yara na wuraren gabashin kasar dake fama da rikice-rikicen yaki. Madam Hillary ta kalubalanci gwamnatin kasar da kuma dakarun sojojin da ba sa ga maciji da gwamnatin kasar da su ajiye makamai da dakatar da rikice-rikicin soji tsakaninsu, ta yadda za a kiyaye 'yan mata da kananan yara marasa galihu don kada a ci zarafinsu.

A gun taron manema labaru da aka shirya, Madam Hillary ta furta cewa, lallai ba za a iya yin hakuri da danyen aikin cin zarafi da akan aikata ga 'yan mata na yankin Goma ba. Ko shakka babu za a yanke hukunci mai tsanani kan duk wadanda suka shafi lamarin cin zarafi. A lokacin da Madam Hillary take yin lacca a Jami'ar Kinkshasa a ranar 10 ga wata, ta bayyana lamarin cin zarafin da ta abku a birnin Goma a matsayin daya daga cikin aikace-aikacen da suka fi muni a tarihin bil adama.

Jama'a masu sauraro, bisa labarin da muka samu an ce, a ranar 11ga wata, Madam Hillary ta kuma kai ziyara a wani barikin soji dake karkarar birnin Goma, inda aka tsugunar da fararen hula kimanin 18,000 wadanda suke neman mafaka sakamakon afkuwar rikice-rikicen soji. Madam Hillary ta yi hira da wassu 'yan mata kai tsaye, wadanda aka ci zarafinsu , inda ta debe musu kewa tare da fadin cewa makasudin rangadinta a Kongo Kinshasa a wannan gami, shi ne don kalubalantar gwamnatin kasar da kuma dakarun sojojin da ba sa ga maciji da gwamnatin kasar da su daina ja-in-ja tsakaninsu a wuraren dake gabashin kasar domin kare 'yan mata na wurin wajen magance cin zarafin da ake yi musu. Kana ta kalubalanci gwamnatin kasar da kuma Majalisar Dinkin Duniya da su yanke hukunci mai tsanani kan wadanda sukan aikata danyen aikin cin zarafi ga 'yan mata da kananan yara.

1 2 3