Ranar 1 ga watan Satumba, a kasar Libya, an kaddamar da bikin tunawa da kafuwar jamhuriyar kasar Libya a shekaru 40 da suka wuce, inda aka shirya gagaruman bukukuwa cikin makon da ya biyo baya. Shugabannin kasashe daban daban sun halarci bikin, haka kuma an shirya wani taron koli na musamman na kungiyar gamayyar kasashen Afirka ta AU a birnin Tripoli, fadar mulkin kasar Libya. Abubuwan sun sa bikin samun wata ma'anar musamman, kamar yadda kafofin watsa labaru suke cewa, Omar Mouammer al Gaddafi, shugaban kasar Libya, yana so ya kara samun kwarjini a gida, da kuma daukaka matsayin kasarsa a Afirka da kuma duk duniya, bisa bukukuwan da aka shirya.
A lokaicn da ake bikin tunawa da kafuwar jamhuriyar kasar Libya, shugaba Gaddafi na kasar ya kira taron koli na musamman na kungiyar AU a Tripoli, bisa matsayinsa na shugaban karba-karba na kungiyar. Sa'an nan ya gayyaci shugabannin kasashe da yawa don halartar bikin da za a shriya a Libya. Duk da cewa yawancin shugabannin kasashen yamma ba su amsa gayyatar ba, amma gayyatar da shugaba Gaddafi ya yi tana da alamun cewa, yana kokarin kyautata matsayinsa a idon mutanen duniya, haka kuma yana so ya nuna matsayin da kasar Libya ke tsayawa a kai na bude kofa , da kiyaye zaman lafiya, da kuma kokarin sauke nauyin da ke kanta.
1 2 3
|