Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-05 14:36:03    
Za a gudanar da dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka

cri

Daga ran 8 zuwa ran 9 ga watan Nuwamba na bana, a birnin Sharm El Sheikh na Masar, za a gudanar da taron ministoci a karo na 4 na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Wannan shi ne gagarumin taro da za a yi bayan taron koli na birnin Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a shekarar 2006, wanda zai kara sada zumunta da hada gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, kuma wata sabuwar ishara ce a tarihin dangantaka tsakaninsu.

Wannan ne taron ministoci a karo na farko da za a yi bayan taron koli na birnin Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a shekarar 2006. Kuma takensa shi ne "Zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da kasashen Afirka a yunkurin samun bunkasuwa mai dorewa". Bangarorin biyu sun dora muhimmanci sosai kan wannan taro. Babban sakataren gwamnatin kasar Masar da ke kula da ayyukan daidaituwar sha'anin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika Ibrahim Ali Hassan ya bayyana cewa, firaministan majalisar gudanarwa na Sin Wen Jiabao da shugaban Masar Mohammed Hosni Mubarak da shugabannin wasu sauran kasashen Afirka da kuma shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka Jean Ping za su halarci bikin bude taron a ran 8 ga wata, tare da wasu jami'ai masu kula da harkokin waje da cinikayya da masana'antu da bunkasuwar tattalin arziki daga kasashen Afirka guda 49.

1 2 3