An yi cikakken bayani kan sauyin hali na tattalin arzikin kasar Sin a gun babban taron nazarin harkokin tattalin arziki na kasar Sin wanda aka rufe shi a ranar alhamis 11 ga wata. Labarin da aka bayar bayan taron ya shafi bangarori daban-daban domin bayyana sauyin halin da ake ciki na tattalin arzikin kasar Sin, ciki hadda ciniki, zuba jari, fitar da kayayyaki, tsarin da ake bi kan masana'antu. Haka kuma ya hada da karfin takara a kasuwanni, makamashi da muhalli, tare kuma da kalubalolin tattalin arziki, tsarin rarraba albarkatun kasa da daidaita harkokin tattalin arziki daga manyan fannoni.
Hakazalika, taron ya gabatar da manyan ayyuka biyar da za a yi ta fuskar tattalin arziki a shekarar badi, wato yin kokarin samun bunkasuwar tattalin arziki cikin karko, gano da sa kaimi ga sabbin hanyoyin samun bunkasuwa, da hazarta yin kwaskwarima kan aikin noma, kyautata tsarin raya tattalin arziki, da karfafa da kuma ba da tabbaci ga ayyukan zaman rayuwar jama'a. (Amina)