in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da gina cibiya mafi girma na jigilar kayayyaki ta layin dogo na kasar Sin
2014-05-06 16:30:08 cri

Bisa labarin da aka samu daga kamfanin kula da jiragen kasa da layin dogo na birnin Guangzhou na kasar Sin, an ce, a 'yan kwanakin baya, kamfanin ya riga ya kaddamar da gina cibiyar ajiye akwatunan da ke dauke da kayayyaki ta hanyar jiragen kasa a Guangzhou, don hada yankin Datian na Guangzhou, da tashar jiragen kasa ta arewacin Guangzhou, da filin jiragen sama na birnin tare, ta yadda mahadarsu za ta zama daya daga cikin manyan cibiyoyin jigilar kayayyaki da ta fi girma a duk nahiyar Asiya.

Kamfanin kula da jiragen kasa da layin dogo na Guangzhou ya gabatar da cewa, bisa shirin da aka tsara, cibiyar akwatunan zai iya jigilar kayayyaki da nauyinsu ya kai ton miliyan 30 a ko wace shekara, sa'an nan tashar jiragen kasa ta arewacin Guangzhou za ta dauki mutane miliyan 57 a ko wace shekara, yayin da filin jiragen sama na birnin zai iya daukar fansinjoji miliyan 100. Bayan kafuwar cibiyar, za a kara hada ta sosai da tashar jiragen kasa ta arewacin Guangzhou, da filin jiragen sama na birnin, ta yadda za a kara inganta kwarewar kasar Sin wajen yin cinikayya da kasashen waje. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China