Bugu da kari, yayin da yake nazari kan matsakacin matsayin kudin da ake kashewa, rahoton ya bayyana cewa, bambancin dake tsakanin kasashe ya ragu, bisa dalilan sabuwar dabarar nazari, da kuma saurin bunkasuwar kasashe masu fama da talauci, wanda ya nuna karin adalci dake ake samu tsakanin kasa da kasa a halin yanzu.
Sabon rahoton da shirin kimanta karfin kasa da kasa na ICP na bankin duniya ya samar, ya kunshi kasashe guda 199. Kuma a matsayin rahoto mafi inganci kan nazarin karfin kudaden kasa da kasa, kullum ana amfani da rahotannin da shirin ICP ya samar a asusun ba da lamuni na duniya IMF da wasu hukumomi daban daban da abin ya shafa. (Maryam)