in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron baje-koli na kasar Sin da kasashen Asiya da Turai karo na 4
2014-09-01 20:35:02 cri

A safiyar yau Litinin 1 ga watan Satumba, a Urumchi, babban birnin jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta kasar Sin, aka bude taron baje-koli na kasar Sin da kasashen Asiya da Turai karo na 4 da kuma taron dandalin tattaunawar yin hadin gwiwa na kasar Sin da kasashen Asiya da Turai dangane da raya tattalin arziki. Mataimakin firaministan kasar Sin Wang Yang wanda ya halarci bikin bude taron tare da yin jawabi mai lakabin "bunkasa shiyyar raya tattalin arziki a hanyar cinikin siliki tare da samun moriyar juna", Wang Yang ya ce, hanyar cinikin siliki ta shafi kasashe fiye da 50, inda akwai mutane kimanin biliyan 3.8, wadda take daya daga cikin shiyyoyi mafiya samun boyayyen karfin bunkasuwa a duk fadin duniya.

Mr. Wang ya bayyana cewa, kasar Sin tana son hada kai da kasashe masu ruwa da tsaki wajen kara bude kasuwanni, da ba da sauki a harkokin ciniki. Sa'an nan kasar Sin tana son kara shigar da kayayyaki masu kyau daga kasashen da hanyar cinikin siliki ta ratsa, musamman ma kayayyakin da ba na albarkatu ba, a kokarin samun daidaito a harkokin ciniki da bunkasuwa mai dorewa.

Har wa yau mataimakin firaministan kasar Sin ya ce, kasar ta karfafa gwiwar masana'antu daga kasashen da hanyar ta ratsa da su shiga ko shirya tarurrukan baje kolin kayayyakinsu a nan kasar Sin, tare da ba su sauki wajen habaka cinikinsu a kasuwar kasar Sin. Kasar Sin in ji shi, tana fatan daddale yarjejeniyar yin cinikayya ba tare da shinge ba tare da karin kasashe da yankunan da hanyar nan ta cinikin siliki ta ratsa, da kuma kyautata manufofin da ke shafar yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China