Bayanin haka ya fito ne sakamakon wani taron dandalin kara wa juna sani game da harkokin zuba jari da sha'anin kudi a tsakanin kasar Sin da nahiyar Afirka na shekarar 2014, da kungiyar kasuwancin kasa da kasa ta kasar Sin da bankin Chartered suka gudanar tare a nan birnin Beijing.
A shekarar 2013, adadin hujjojin da kasar Sin ta fitar zuwa Afirka ya kai dallar Amurka biliyan 92.8, adadin da ya karu da kashi 8.8 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2012, yayin da adadin hujjojin da aka shigo da su daga kasashen Afirka ya kai dallar Amurka biliyan 117.4, adadin da ya karu da kashi 3.8 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2012. Har ila yau an bayyana cewa, yawan jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba a Afirka na ci gaba da karuwa. Ya zuwa yanzu dai an riga an kafa kamfanonin zuba jari a Afirka sama da dubu 2, wadanda suka shafi ayyukan noma, kayayyakin more rayuwa, sarrafawa, hakar ma'adinai, sha'anin kudi, kasuwanci da dai sauransu. (Maryam)