A cikin bayanin, an yi nuni cewa, yiwuwar aukuwar rikicin tattalin arziki a kasar Sin ba ta da girma. Na farko, dukkan rancen kudin da Sin take bi na cikin gida ne, sauyin yanayin hada-hadar kudi na kasashen waje ba zai yi tasiri ga kasar Sin ba. Na biyu, ba a amfani da rancen kudi da kadarori a matsayin hannayen jari a cikin tsarin hada-hadar kudi na Sin. Na uku kuwa, kudin da jama'ar Sin suka ajiye a bankuna ya karu, ta haka bankuna za su iya bayar da isassun rancen kudi. Na karshe, kasar Sin tana da kudaden kasashen waje, duk da cewa manufofin da Amurka ta janye kanta daga cikin, hakan ya kawo cikas ga fitar kudi zuwa kasashen waje, amma hakan ba zai yi tasiri ga kasar Sin ba. (Zainab)