Hanyar rage saurin bunkasuwar tattalin arziki ta dace da zabin kasar Sin na nufin neman dauwamammen ci gaba
Kakakin asusun bada lamuni na duniya wato IMF Gerry Rice ya bayyana cewa, rage saurin bunkasuwar tattalin arziki na kasar Sin aiki ne da ya dace wajen daidaita da neman dauwamammen ci gaba da shiga cikin kasashe masu arziki na duniya. Ya ce, ko da yake ana samu raguwar saurin bunkasuwar tattalin arziki a kasar Sin, amma tattalin arzikin Sin ya fi samun ci gaba idan aka kwantanta da sauran kasashen duniya.
Mr. Rice wanda ya bayyana hakan a gun taron manema labaru a wannan rana, ya ce, kamar yadda rahoton IMF game da tattalin arzikin Sin a wannan shekara ya nuna, an iya amincewa da tsara burin samun bunkasuwar tattalin arzikin Sin da kashi 6.5 cikin dari zuwa 7 cikin dari bayan shekarar 2015.
A ganin IMF, kasar Sin ta iya amincewa da wasu raguwar saurin bunkasuwar tattalin arzikin ta, wannan yana da muhimmanci gare ta wajen warware wasu matsaloli da kyautata tsari yayin da take kokarin samun bunkasuwa. (Zainab)