An bayyana kasar Sin a matsayin ginshikin ci gaban tattalin arzikin duniya. Duk kuwa da cewa jimlar kudaden da kasar ta Sin ta samu daga aikin kawo alfanu gida wato GDP ya dan ragu, amma har ya zuwa yanzu kasar Sin na yin muhimmin tasiri a fannin ci gaban tattalin arziki, da cinikayyar dake wakana a dukkanin sassan wannan duniya.
Wani masani a fannin tattalin arziki dake aiki da kamfanin HIS Global Insight mai suna Brian Jackson ne ya bayyana hakan, cikin wani sharhi da jaridar People's Daily ta nan kasar Sin ta buga a Larabar nan. Kaza lika Mr. Jackson ya kara da cewa, ko da yake tattalin arzikin kasar Sin ya samu koma baya na dan lokaci, a hannu guda gwamnatin kasar na da isasshen kasafin kudi da ke sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikinta.
A cewarsa, cikin dan lokaci a nan gaba, za a samu 'yan kwadago mazauna garuruwa dake da ilmi, da kuma dimbin 'yan cin rani na yankunan karkara, wadanda za su zama muhimmin karfi wajen kara azama ga karuwar tattalin arzikin kasar.
Bugu da kari, sharhi na Jackson ya karfafa cewa, a baya bayan nan, basussuka da kasuwar gidajen kwana ne matsaloli biyu, da ke gaban kasar Sin ta fuskar tattalin arziki, wadanda kuma ka yi illa ga harkokin zuba jari.(Kande Gao)