in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangaren masana'antun Sin ya karu a watan Afrilu
2014-05-01 16:03:43 cri
Bayanai a hukumance na nuna cewa, bangaren masana'antun kasar Sin ya ci gaba da karuwa a watan Afrilu,inda a ranar Alhamis aka samu sabbin shaidu da ke nuna ci gaban bangaren masana'antun kasar.

Wata sanarwa da hukumar kididdiga da kuma sashen kula da kayayyakin kasar suka bayar,ya nuna cewa ,alkaluman sayar da kayayyaki PMI na bangaren masana'antun kasar ya karu zuwa kashi 50.4 cikin 100 a watan da ya gabata daga kashi 50.3 cikin 100 a watan Maris.

Wannan shi ne karo na biyu cikin wata guda a jere da ake samun karuwar wadannan alkaluma,wadanda suka fara karuwa tun a watan Maris bayan da suka sauka kasa a cikin watanni uku.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China