in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ribar da manyan masana'antu mallakar gwamnati da masana'antu masu zaman kansu suka samu ta karu da kashi 11.4 cikin dari a farkon rabin wannan shekara
2014-07-27 17:37:25 cri

Yau ranar Lahadi 27 ga wata, hukumar kididdigar kasar Sin ta gabatar da adadin masana'antu a hada-hadar kudi, wadda ta nuna cewa, a farkon rabin wannan shekara jimillar ribar da masana'antu mallakar gwamnati da masana'antu masu zaman kansu da suka iya samun ribar kudin Sin yuan fiye da miliyan 5 daga kayayyakin da suka sayar, ta kai yuan biliyan 2864 da miliyan 980, adadin da ya karu da kashi 11.4 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar bara. Galibi dai ribar da aka samu a fannin masana'antu karuwa take yi ba tare da tangarda ba.

Adadin ya kuma nuna cewa, a watan Yunin nan, jimillar ribar da masana'antu mallakar gwamnati da masana'antu masu zaman kansu suka samu da ya kai kudin Sin yuan fiye da miliyan 5 daga ribar kayayyakinsu, ta kai yuan biliyan 588 da miliyan 80, wadda ta karu da kashi 17.9 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar bara, kuma saurin karuwar ya karu da kashi 9 cikin dari bisa na watan Mayun da ya gabata.

Masu sharhi na ganin cewa, muhimman dalilan da suka haifar da saurin karuwar ribar a watan Yuni su ne saurin karuwar sayayya, dan raguwar kudaden da aka kashe wajen kera kayayyaki, da kyakkyawar rawar da sana'o'i kalilan suka taka da dai sauransu. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China