Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD Mista Wang Min ya bayyana a ranar 12 ga wata a hedkwatar MDD da ke birnin New York cewa, sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki ya zama wata hanyar da ake bi a cikin dogon lokaci wajen daidaita matsalolin tsakiyar yankin Afirka.
Mista Wang ya yi wannan bayani ne a gun taron bainar jama'a da aka shirya kan aikin da ofishin MDD da ke tsakiyar yankin Afirka da batun dakarun "Lord's Resistance Army", wanda aka shirya a ran nan.
Wang ya yi nuni da cewa, aikin daidaita matsalolin da ake gamuwa da su a tsakiyar yankin Afirka, wata hanya ce da ake bi cikin dogon lokaci, don sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki. Bunkasuwa ta zama wani tushe mai samun zaman lafiya cikin dogon lokaci, rashin bunkasuwa yana daya daga cikin manyan dalilan da ke haddasar rikici a nahiyar Afirka. Ya kamata a girmama ikon jagorancin kasashen Afirka wajen raya kansu. A yayin da kasashen suke bayar da taimako ga tsakiyar yankin Afirka, ya kamata kasashen duniya su saurari ra'ayoyin kasashen Afirka da girmama su, da hada kai da su da yin mu'ammala da kungiyoyin Afirka, don kara kwarewarsu, wajen daidaita matsalolinsu bisa karfin kansu. (Danladi)