Yayin taron, Mr Xi ya jadadda cewa, samun ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire wani tsari ne da ke sa kaimi ga aikin yin kirkire-kirkire musamman ma a fannin kimiyya da fasaha, tare kuma da nacewa ga hanyar biya bukatun jama'a da bunkasa sana'o'i daban-daban. Sannan kuma in ji shi ya kamata a tabbatar da matsayin kamfani na bada jagoranci a ayyukan kirkire-kirkire, da rarraba albarkatun kasar yadda ya kamata bisa tsarin kasuwa da yin amfani da fifikon tsarin gurguzu, har ma da kara karfin kimiyya da fasaha don samun ci gaban tattalin arzikin kasar. (Amina)