Lou Jiwei wanda ya yi bayani kan yanayin da kasar Sin take ciki ta fuskar tattalin arziki a gun taron, ya ce ana samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar yadda ya kamata, amma ana fuskantar matsin lamba na sassauta saurin bunkasuwar tattalin arziki a nan gaba. Bisa wannan hali, yace za a ci gaba da maida hankali kan fannoni daban daban yayin da gwamnatin Sin take tsara manyan manufofin tattalin arziki, musamman a fannin samar da karin guraben aikin yi da tabbatar da farashin kaya a kasar, kuma ba za a yi babbar kwaskwarima kan manufofin domin canzawar wani ma'aunin tattalin arziki kadai ba.
Lou Jiwei ya kara da cewa, game da manufofin kudi na kasar Sin, gwamnatin kasar ta dauki matakai uku don sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar, da suka hada da Na farko, kara rage harajin da ake karbar daga wajen kananan kamfanonin kasar. Sai na biyu sa kaimi ga yin amfani da jari daga al'ummar kasar wajen gina ayyukan more rayuwa da samar da makamashi mai tsabta bisa yin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin kasar da al'ummarta. Sannan na uku kuma shi ne ci gaba da yin kwaskwarima don kara sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar a nan gaba. Hakazalika kuma, ministan kudin na kasar Sin ya ce gwamnatin kasar tana kara yin kwaskwarima kan kamfanonin mallakar gwamnati, tsarin rajistar iyalai, da gonaki da filayen kauyuka da sauransu don kara raya tattalin arzikin kasar. (Zainab)