Kakakin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin Shen Danyang ya bayyana a Litinin din nan 18 ga wata cewa, shekaru shida bayan da kasar ta fara gudanar da dokar yaki da babakere, kamfanonin da aka bincika sun hada da na gida da kuma na waje. Wannan doka in ji shi ba wai kawai ana gudanar da ita kan kamfanonin ketare ba ne, ko wane kamfani na da ikonsa iri daya a gaban kotu. Mr Shen ya ce bayyana haka da yayi ya biyo bayan damuwa da kafofin yada labaru suke da shi kan wannan batu.
Mr Shen ya kara da cewa, hukumomin dake da nasaba da wannan batu na gwamnatin kasar Sin sun yi bincike bisa doka kan wasu kamfanoni da ake shakkun sun yi babakere, yace hakan wani muhimmin mataki ne wajen ba da tabbaci ga yin takara cikin 'yanci da kiyaye moriyar masu sayayya. Matakin kuma da kasa da kasa su kan gudanar da shi, duk wani kamfani na gida ko na jarin waje da ya karya wannan doka za a yanke masa hukunci. (Amina)