Ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta kira wani taron manema labarai a baya bayan nan, inda kakakin ma'aikatar Shen Danyang ya furta cewa, yawan kudi da ake samu ta hanyar cinikayya ta yanar gizo, ya kai Yuan biliyan 1850 a shekara ta 2013 kadai, wanda ya sanya kasar ta Sin haye matsayin koli a duniya a fannin hada hadar cinikayya ta yanar gizo.
Haka kuma a watanni biyar na bana, jimillar kudin da aka samu ta hanyar cinikayya ta yanar gizo ta karu da kashi 32.5 cikin dari, bisa na makamancin lokaci a bara, ana kuma hasashen saurin karuwar wannan adadi a nan gaba.
Yayin da ake samun saurin bunkasuwa, an kuma gano wasu matsaloli a fannin yin cinikayya ta yanar gizo, kamar zamba ta yanar gizo, da sayar da kayayyakin jabu ko marasa inganci, da kuma tono bayanan siri na masu sayayya. Ganin haka, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta hada kai tare da kwamitin kula da harkokin kudi na majalisar dokokin kasar wajen tsara dokar cinikayya ta yanar gizo, da ka'idojin da suka jibanci hakan. (Kande Gao)