in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta raya tattalin arzikinta ta fannoni 8
2014-12-05 21:42:19 cri

A yau ne hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS ta kira wani taro domin tantance da nazarin hanyoyin inganta tattalin arziki da za a yi a shekara mai zuwa, inda aka bayar da muhimman matakan yadda za a raya tattalin arzikin kasar.

Da farko wajibi ne kasar Sin ta dace da sabbin sauye-sauyen da za a samu ta fuskar bunkasuwar tattalin arziki. Na biyu tabbatar da ci-gaban tattalin arzikin kasar ba tare da tangarda ba tare da kyautata tsarin tattalin arziki yadda ya kamata. Na uku, dole ne a bunkasa sabbin sana'o'i da sana'ar ba da hidima bisa manyan tsare-tsare. Na hudu, tilas ne a gaggauta sauya hanyar raya aikin gona. Na biyar kuma, wajibi ne a kyautata bunkasar tattalin arziki a sassa daban daban na kasar Sin, musamman ma zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, zirin tattalin arziki na kogin Yangtse, da biranen Beijing da Tianjin da lardin Hebei. Na shida kuwa, dole ne a mai da hankali kan samar da guraben aikin yi da yaki da talauci. Na bakwai, wajibi ne a ci gaba da yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arzikin kasar. Na takwas kuma wajibi ne a yi kokarin samun daidaito a harkar shigi da fice ta fuskar cinikin waje.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China