in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Sin zai karu da kimanin kashi 7.4 bisa dari a shekarar 2014
2014-04-30 10:27:18 cri
Bisa rahoton da cibiyar nazarin ilimin kimiyyar zamantakewa ta kasar Sin ta fitar game da makomar tattalin arzikin kasar Sin a ran 29 ga wata a nan birnin Beijing, an ce, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin a shekarar nan ta 2014, zai kai kashi 7.4 bisa dari, adadin da ya dan ragu idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.

Cikin wannan rahoto, an ce, cikin shekaru 30 da suka gabata, matsakaicin adadin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya kai kimanin kashi 10 bisa dari, wanda ya sa karfin tattalin arzikin ya kasance a matsayi na biyu tsakanin daukacin kasashen duniya. Haka kuma saurin karuwar tattalin arzikin kasar na shiga wani sabon lokaci a bana, inda bisa hasashen da cibiyar ta yi, saurin karuwar sa zai kasance kashi 7.5 bisa dari cikin shekaru da dama masu zuwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China