A yau alhamis 17 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin madam Hua Chunying ta bayyana cewa, bunkasuwar tattalin arzikin Sin ta taka rawar a zo a gani wajen bunkasa tattalin arzikin duniya.
Tayi bayanin cewa GDPn kasar ya karu da kashi 7.4 cikin dari bisa makamancin lokaci a farkon watanni uku na bana, wanda ya yi kasa kadan bisa hasashen bana na karuwa da kimanin kashi 7.5 cikin dari. Wasu kafofin yada labarai sun yi sharhin cewa, watakila wannan zai janye saurin karuwar tattalin arzikin duniya, a game da hakan, madam Hua ta bayyana a wajen taron manema labaru a yau cewa, a cikin jawabinsa a gun bikin bude taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar Asiya na Bo'ao da aka kammala kwanannan, firaministan Sin Li Keqiang ya gabatar da yanayin da Sin ke ciki wajen bunkasa tattalin arziki. Inda ya ce, bayan shekaru sama da 30 da bunkasa shi cikin sauri, yanzu tattalin arzikin Sin ya riga ya shiga wani sabon mataki na neman kyautata inganci.(Fatima)