An yi bikin cika shekaru 69 da samun nasarar turjiya kan harin Japan a birnin Nanjing na kasar Sin
Ranar 15 ga watan Agusta rana ce da Japan ta sanar da mika wuyanta, kuma a wannan karon ya cika shekaru 69 da samun nasarar turjiya kan harin Japan da kuma yaki da ra'ayin nuna karfin soja. A safiyar wannan rana masu kaunar zaman lafiya na gida da na waje sun taru a cibiyar tunawa da 'yan uwan da suka mutu sakamakon kisan kiyashi da Japan ta yi, domin nuna ta'aziyya ga wadanda suka mutu a kisan da yawansu ya kai 300,000 tare da fatan wanzar da zaman lafiya a duniya.
Shugaban wannan cibiya Zhu Chengshan ya bayyana cewa, masu ra'ayin zaman lafiya a gabashi da arewacin Asiya na ba da gudunwama sosai wajen shimfida zaman lafiya a Asiya, Sinawa, 'yan kasar Japan da Korea ta kudu sun taru a wannan karo da zummar yin kira da a hana tada yaki da kiyaye zaman lafiya, tare kuma da mutunta hakikkanin tarihi da samun bunkasuwa nan gaba. (Amina)