A birnin Beijing, mutane da dama sun yi bukukuwa fiye da 40, da zummar tuna wannan rana na bakin ciki a tarihi da kuma saka kishin kasa a zukatan al'umma.
Wakilai kimanin 100 daga kungiyoyi daban-daban na yankin Hong kong sun yi zanga-zanga a kofar ofishin jakadancin kasar Japan dake Hong kong domin bayyana rashin jin dadinsu na shawarar da Japan ta yanke na maido da ikon daukar matakan soji, da gyara abubuwan dake cikin litattafan tarihi na makarantu yadda ta ga dama, da mamaye tsibirin Diaoyu na kasar Sin, inda suka nemi gwamnatin Japan da ta amince da gaskiyar laifukan da ta aikata da rogon gafara daga kasashen da ta taba kai ma hari. (Amina)