in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kebe ranar tunawa da kisan kiyashin Nanjing
2014-02-27 14:34:00 cri
Kasar Sin za ta kafa dokar da za ta tanadi kebe rana ta musamman, domin tunawa da nasarar yaki da harin Japanawa, tare da ranar tunawa da kisan kiyashin birnin Nanjing.

Game da hakan, shahararren masanin kasar Amurka, kuma shehun malami Xiong Jie, na ganin cewa, gwamnatin kasar Sin ta dauki wannan mataki ne, a matsayin gargadi mai tsanani ga firaministan kasar Japan, da wasu jami'an gwamnatinsa game da yawan kai ziyara a haikalin Yasukuni, inda aka ajiye alluna da ke dauke da sunayen masu laifuffukan yakin duniya na 2, da kuma ra'ayin da suke da shi na watsi da ainihin tarihi.

Xiong Jie ya bayyana cewa, wannan matakin da gwamnatin kasar Sin ta dauka na kebe wadannan ranaku guda biyu, ta hanyar kafa doka na da ma'ana sosai a fannoni guda biyu. Da farko, ana fatan tunawa da mazan jiya wadanda suka sadaukar da kai yayin yakin, da wadanda suka ba da gudunmawa, da yawan Sinawa da suka rasa rayukansu sakamakon kisan gillar da sojojin Japan suka yi. Na biyu, gwamnatin Sin ta yi hakan ne don yin gargadi ga shugabannin gwamnatin Japan, tare da taimakawa kasashen duniya, wajen kara fahimtar yadda harin da Japan ta yi wa Sinawa ya wakana, da kuma dalilin da ya sa gwamnatin Sin ke adawa da kai ziyara haikalin Yasukuni da shugabannin Japan suke yi. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China