Cikin sharhinsa, Mr. Xia ya bayyana cewa, har yanzu, gwamnatin Shinzo Abe ba ta amsa laifuffukan da kasar ta aikata cikin tarihi ba, inda ta sha ta kai ziyara wurin ibadar Yasukuni da ake takaddama a kai, da ta kebe kaburburan masu laifukan yaki, ciki hadda wadanda suka jagoranci dakarun kasar yayin yakin duniya na biyu, lamarin da ya bata ran jama'ar kasar Sin sosai, wanda kuma ya kawo barazana ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Mr. Xia ya kara da cewa, a halin yanzu, kasar Japan ita ce kasa mai samun bunkawuwar tattalin arziki, ana iya fahimta cewa, kasar tana da wani buri na siyasa, amma, idan tana son daukar alhakin shimfida zaman lafiya da na karko na kasa da kasa, ya kamata ta samu amincewar gamayyar kasa da kasa, musamman ma kasashen dake makwabtaka da ita. Kana, a halin yanzu, gwamnatin kasar Japan dake karkashin jagorancin Shinzo Abe na kokarin musanta bayanan tarihi, wannan zai haddasa illa ga kasarta, kuma ya kamata gamayyar kasa da kasa su mai da hankali kan wannan batu. (Maryam)